Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana bincike kan lamarin wata mata mai shekaru 18 ‘yar asalin kasar Saudiyya, wacce ta tsere zuwa kasar Thailand, ta kuma kulle kanta a wani dakin otel da ke filin tashin jiragen kasar.
Rahaf Mohammed Al- Qunun, ta isa birnin Bangkok a ranar Asabar din da ta gabata a wani jirgin da ya taso daga Kuwaiti, bayan da ta tserewa iyalanta, inda ta yi ikarin cewa, za su kashe ta idan ta koma gida.
Lamarin matashiyar ya ja hankalin duniya, bayan da ta shiga shafukan sada zumunta, ta yi ta wallafa hotuna da rubuta kan halin da take cikin daga inda take boye.
Hakan ya janyo hankulan hukumomin kasar ta Thailand, inda suka sauya shirinsu na mayar da Rahaf gida.
A cewar, shugaban hukumar shige da fice a kasar ta Thailand, Surachate Hakpan, “a yau hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, sun fada min cewa, zai dauki kwanaki biyar kafin su duba bukatar da ta gabatar ta neman mafaka, sannan zai dauki wasu kwanakin biyar a yi shirye-shiryen tafiyarta.”
Tun bayan kisan dan jarida Jamal Khashoggi, kasashen duniya sun yi ta sa ido kan yadda ake take hakkokin bil Adama a kasar.
Facebook Forum