Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Taimaka Wa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Kan Harkokin Yada Labarai, Isa Mohammed, Ya Rasu.


Sanata Ahmed Lawan
Sanata Ahmed Lawan

Kungiyar 'yan Jarada a Najeriya (NUJ), na makokin rasuwar daya daga cikin hamshakan mambobinta, Mai Taimaka Ma Shugaban Majalisar Dattawa Kan Harkokin Yada Labarai.

Mai Taimakawa Na Musamman Ma Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Kan Harkokin Yada Labarai, Malam Mohammed Isa, ya rasu ranar Jumma’a, a cewar kafafen yada labarai, ciki da Premium Times.

Ola Awoniyi, Mai Bayar Da Shawara Na Musamman Ga Shugaban Majalisar Dattawa Kan Harkokin Yada Labarai, ya bayyana a Abuja jiya Asabar cewa, Malam Isa ya rasu ne yayin da ake masa jinyar raunukan da ya ji bayan wani hatsarin mota da ya yi a kan hanyar Mina zuwa Abuja a jihar Neja.

Mr. Awonyi ya ce tuni aka yi jana’izar mamacin a Funtua, jihar Katsina kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A halin da ake ciki, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya yi ta’aziyya ga iyalai, da abokan aikin mamacin. Ya kuma yi ta’aziyya ma Kungiyar ‘Yan Jaridar Najeriya (NUJ) kan wannan babban rashin. Haka zalika ya yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar Katsina da jama’ar jihar baki daya, saboda da rasuwar Malam Isa.

-PremiumTimes

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG