Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morgan Tsvangirai, Madugun Adawar Zimbabwe, Ya Rasu


Morgan Tsvangirai
Morgan Tsvangirai

Madugun adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, wanda yayi suna a saboda jajircewar da ya jima yana yi ta neman kawo karshen mulkin shugaba Robert Mugabe, ya rasu 'yan watanni kadan a bayan da Mugabe ya sauka daga kan mulki.

Gwagwarmayar da ya sha yi a tsawon shekaru 65 da yayi a duniya ta yi tasiri wajen janyo ajalinsa jiya laraba a Afirka ta Kudu, bayan ya jima yana fama da cutar sankara.

Mataimakin shugaban jam'iyyar MDC, Elias Mudzuri, ya tabbatar da mutuwar Mr. Tsvangirai jiya laraba da maraice, yana mai fadin cewa iyalan marigayin da bakinsu sun bayyana masa hakan.

Har ya zuwa lokacin da ya kusan barin duniya, Mr. Tsvangirai bai ja kafa a gwagwarmayarsa ta neman kawo sauyin siyasa a kasar Zimbabwe ba.

Wannan haka ta sa ta cimma ruwa jim kadan kafin rasuwarsa, inda a karshen shekarar 2017 MUgabe yayi murabus bayan mulkin shekaru 38.

Allah bai ba Tsvangirai ikon jagorancin jam'iyyarsa ta MDC wajen samun nasara a Zimbabwe ba, amma magoya bayansa suka ce kokari da kuma gwagwarmayar da yayi ita ce a'ala.

Wani dan jam'iyyar MDC mai suna Austin Moyo, yace "Morgan Tsvangirai shine mutumin farko da yayi ta-maza ya fito ya kalubalanci Mugabe, kuma ya haddasa samun sauyi."

Tun shekarar 2016 Tsvangirai yake fama da cutar sankara ta dubura, wadda a wasu lokuta take kama da cutar basur.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG