Wata mata ‘yar shekaru 43 da haihuwa ta bada labarin irin bajintar da ta yi domin kwatar Kanata daga hannun wani matashi dan shekaru 30 da haihuwa wanda ya shigar mata gida cikin dare da niyyar yi mata sata.
Ms Karen Dolley ta ce wasan karetin da ta koya a lokacin da take makarantar sakandire ne ya taimaketa har ta kaiga kama wannan barawo ta kuma haninta shi ga jami’an tsaro.
A yayin da wannan matashi ya shigar mata gida, Dolley tana tsakar bacci sai taji motsi a cikin dakin ta, koda ta bude ido sai ta ga ashe matashinne ke neman abin da zai sata ita kuma tai maza maza ta daka tsalle daga kan gadon ta inda suka fara artabu da wannan matashi.
Da farko ta yi ta kai mai nushi yana kauce wa har ta sai da ta sami nasarar tura shi ga kwanar daki har sai da matashin yayi nadama.
Dolley ta kara da cewar matashin ya yi kokarin kamata da kokowa amma bata bari yayi kusa da it aba, ta bayyana cewar tana da wata takobi irin wadda ake wasan kareti a kasar japan da ita a kusa da gefen gadon ta, Da wannan takobi ta tare matashin har saida ‘yan sanda suka iso gidan sannan ta hanunta shi ga jami’an tsaron.