Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikaciyar Bogi Ta Yi Allura An Mutu


An yanke ma wata ma'aikaciyar lafiyar bogi hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari sakamakon hallaka wata mata da ta yi a yayin da ta gabza mata wata allura wadda tazo da tangarda.

Ma'aikaciyar mai suna Taibat Jegede wadda aka fi sani da Alhaja, ta yi ma mamaciyar mai suna Seyi Ibitoye allura ne a yayin da take kokarin zubar mata ciki ne kamar yadda kotun ta ce shaidun sun bayyana.

Mai shari'a Femi Onipede ta ce wannan shine karo na biyu da da ma'aikaciyar ta aikata irin wannan mugun laifi, kuma ta kara da cewa wanna lokacin shaidu shidda sun bada tabbacin cewar mamaciyar tayi ta zubda jini bayan allurar da aka yi mata wadda hakan yayi sanadiyyar rayuwar ta.

Mai shari'ar ta bada cikakken bayanin cewar ma'aikaciyar ta bogi ce domin kuwa bata kammala karatun da ta fara a makarantar koyon aikin jiyya dake Akure a sakamakon rashin kokari da faduwa jarabawa.

Bayanai daga shaidun sun nuna cewar ma'aikaciyar bogin ta kwana biyu tana ba mamaciyar magunguna a yayin da ta nuna mata cewar tana fama da zubar jini, haka kuma ta yi kokarin bata magungunan ciwon jiki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG