Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar kwadagon Najeriya ta tilastawa ma'akatan wutar lantarki shiga yajin aiki


Layin wutar lantarki
Layin wutar lantarki

Harkokin yau da kullum sun tsaya cik a ofisoshin ma'aikatan wutar lantarki sanadiyar yajin aikin dole da kungiyar kwadago ta sasu shiga alatilas

Tunda sanyin safiyar yau ne wakilan kungiyar kwadagon Najeriya aduk fadin kasar suka yi diran mikiya akan ofisoshin ma'aikatar samarda wutar lantarki saboda karin kudin wutar da aka yi.

Wakilan sun tabbatar cewa hada-hada irin na yau da kullum basu gudana ba a duk fadin kasar lamarin da ya sa wadanda suke je sayen katin wuta kokuma biyan kudi basu samu yin hakan ba..

Kungiyar ta hana ma'aikatan shiga ko fita daga ofisoshinsu.

Wani daga cikin shugabannin kungiyar kwadago yace sun dauki matakin ne domin tilastawa kamfanonin wutar lantarki su janye karin da suka yi daya ga wannan watan domin a wasu wuraren babu karin samun wutar lantarki. Yace kara kudin ba adalci ba ne a irin yanayin da mutane ke ciki.

Wasu da aka zanta dasu sun ce kafin a kara kudin wuta kamata ya yi a samu karin wutar. Suna cewa shi talaka da yake fama da yadda zai samu abinci yaci ba shi ne za'a karawa kudin wuta ba. Suna kiran gwamnati da ta yiwa Allah ta ji tausayin wahalar da talaka ke sha ta mayar da kudin wuta yadda yake da can.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG