Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Jahar Naija Ta Ce Shekarun Wani Matashi Sun Yi Kadan A Takara


Court Nigeria
Court Nigeria

Wata sabuwar takaddamar siyasa da ta kunno kai a jahar Naijan Najeriya ta shafi wani matashi mai suna Murtala Badaru, wanda ya tsaya takarar siyasa a karkashin jam’iyar APC domin zama dan Majalisar Wakilan jahar, wanda kamar yadda kafar sadarwar Naij.com ta ruwaito, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya doke abokin takararsa Shu’aibu Iya na jam’iyyar PDP.

Sai dai kuma abokin takarar tasa karkashin jam’iyyar PDP, ya fito karara ya soki zaben da aka yi ma Badaru da cewa bai cancanci zaben da aka yi masa ba, inda ya bada dalilan cewar Murtala Badaru ya yi amfani da takardun karya kuma ya kara da cewar shekarun dan takarar ba su kai adadin shekarun da ya kamata a ce ya fito a wannan matsayi ba.

A wani zama da kotun jin kararrakin zabe ta yi jiya Talata, 6 ga wannan watan, Mai Sharia’ Olatunde Oshdi ya wanke dan takarar daga zargin yin anfani da takardun bogi kamar yadda abokin takararsa Shu’aibu Iya ya bayyana ma kotun.

Mai Shari’ar ya bayyana soke zaben da aka yi ma Badaru a sakamakon cewar shekarun sa ba su kai talatin ba kamar yadda shari’a ta tanada, dan haka Mai Sahiri’ar ya ba hukumar zabe ta kasa umurnin ta sake shirya wani sabon zabe a cikin kwanaki tasa’in.

A yanzu haka dai lauyan dan takarar ya ce za su daukaka kara.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG