Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe 6 Ne Ke Taro A Kasar Pakistan Domin Hada Kai Su Yaki 'Yan Taadda


NIGER: Taro kan dokokin ma'adanai
NIGER: Taro kan dokokin ma'adanai

Kasashen da suka hada da Pakistan, China,Russia,Turkey,Afghanista,da Iran suna gudanar da taro a kasar Pakista domin duba yada zasu hada kai su yaki 'yan taadda.

Yanzu haka kasashe 6 ne suka fara wani taro a Pakistan domin duba yadda zasu tuinkari kalubalen ayyukan taaddanci da kuma hadin kai tsakanin su.

Kakakin majilisar dokokin kasashen Pakistan, China,Russia,Turkiyya,Afghanistan, da Iran, sune ke jagorantar tawagar kasasahen su wajen wannan taron.

Kuma ana gudanar da taron ne karkashin tsastsauran matakan tsaro a babban birnin kasar na Pakistan.

Shugaban majilisar dattawan kasar Pakistan Raza Rabbani yayi anfani da wannan taron wajen mayar wa gwamnatin Amurka Martani

Rabbani yace sun gani a cikin ‘yan kwanaki biyu da suka gabata mataimakin shugaban kasar Amurka har yana da kwarin gwiwar da ikon cewa ya saka kasar Pakistan a ciki kasashen da ake sawa ido,

Shugaban majilisar yace to bari ya fadi da babban murya kuma duniya ta saurara Pakistan kasa ce me cikakken ‘yancin cin gashin kai.

Haka kuma yace kasar bata karban umurni daga hannun kowa, balle ma Amurka.

Wadannan kalamai na Rabbani dai suna nufin amsa ce kai tsaye ga kalaman Mike Pence.

A lokacin da yake wa sojojin Amurka jawabi sailin da yakai ziyara a Afghanistan ranar alhamis.

An jiwo Pence nacewa Pakistan ta jima tana baiwa ‘yan taadda irin su Taliban da sauran kungiyoyin ‘yan taadda mafaka.

Awannan taron gwamnatin kasar Pakistan tayi anfani dashi domin mayar wa Pence da martini.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG