Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru na shirin taso keyar 'yan Najeriya dubu 56 dake gudun hijira


Sansanin 'yan Najeriya masu gudun hijira a Kamaru
Sansanin 'yan Najeriya masu gudun hijira a Kamaru

Hukumomin Kamaru sun ce cikin kwanakin nan zasu tasa keyar 'yan Najeriya su dubu 56 dake gudun hijira a kasarsu zuwa gida Najeriya sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram.

Batun taso keyar 'yan Najeriyan zuwa gida na tada hankalin mahukunta a kasar saboda tanadin da ya kamata su yi kafin mutanen su iso.

Amma tuni majalisar wakilan tarayya ta kafa kwamitin aiki da cikawa da ya kunshi wakilai daga shiyar arewa maso gabashin Najeriya dake cikin majalisar. Su ne zasu je kasar Kamaru domin tattaunawa da mahukuntar kasar ta Kamaru.

Onarebul Lawal Garba yana cikin kwamitin kula da 'yan gudun hijiran na majalisar wakilan ya kuma bayyana matakan da zasu dauka domin dawo da 'yan Najeriyan.

Yace sun tattauna batun a majalisa. An kafa kwamitin mutanen da zasu je Kamaru tare da duk 'yan majalisar wakilan da suka fito daga yankin arewa maso gabas.

Akwai wani kwamiti kuma da zai tafi Bakasi. Zasu kuma sadu da gwamnan Adamawa saboda ta jiharsa ce za'a kawo 'yan gudun hijiran.

Su ma 'yan majalisar dattawa lamarin ya tayar masu da hankali kamar yadda Sanata Abdulaziz Murtala Nyako ya bayyana. Yace kamar Kamaru ta yi dan gaggawa. Kamata ya yi ta karawa Najeriya dan lokaci amma zasu ga yadda zasu taimaka.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG