Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaruma Aishwarya Ta Dawo a Cikin Sabon Fim Din Jazbaa


Aishwarya Rai Bachchan
Aishwarya Rai Bachchan

A ya’u Bollywood zata fito da fim din da aka dade ana jira mai suna JAZBAA, Aishwarya Rai Bachchan da Irrfan Khan, duk sun fito a wannan fim din.

Wannan fim din dai shine shifidan dawowar Ash wace ta kwashe shekaru biyar tana hutu batare da fitowa a kowane fim ba, jama’a da dama a kasar Indiya, suna cike da farin ciki ganin cewa tauraruwar da suke sha’awa ta dawo faggen fina finai.

Masu dawainiyar nuna fim din Akshaye Rathi, ya ce fim din JAZBAA, fim ne mai bansha’awa da kayatarwa, kuma akwai ruwar yana iya kasancewa a sahun gaban fina finai.

Ya ce kasancewar fitattun jarumai biyu Aishawarya Rai Bachchan da Irrfan Khan, zai sa fim din yayi tasiri da kima a idon jama’a, a faggen fina finai a gida da waje saboda abubuwan da fim din ya kunsa da kuma wakokin da aka yin amfani dasu a cikin fim din.

Game da kudaden da aka kashe wajen gudanar da fim din Akshaye, ya ce baki daya abunda aka kashe Dalar Amurka 5,100, kuma ba zai gagarar maida wa a cikin dan karamin lokaci ba.

Yana kuma harsashen cewa labarai na fatar baki dangane da fim din daga jama’a, zai taimakawa fim din.

Dallatar da fim din ta tauraron dan Adam, wato Satalite da kuma sayarda wakokin fim din zai taimaka wajen Karin kudin shiga.
Da yake Magana akan dawowar Ash, bayan shekaru biyar ya ce jaruma ce wace ba za’a manta da it aba.

Ya kara da cewa alal hakika, jarumai kamar su Aishwarya, Madhuri Dixit da rani Mukerji, fitattu ne idan irunsu suka dawo nasara ce ga fim din da suka fito a ciki.

XS
SM
MD
LG