A ‘Yan kwanakin nan ne dai wasu mutane suka kai wa wasu al’umma a birnin Asaba dake jihar Delta farmaki, inda mutane 4 suka rasa rayukkansu, wasu kuma suka jikkata.
Sai dai kuma jami’an tsaron dake yankin kudu-maso-gabashin Nigeria sunce a tsaye suke domin dawo da zaman lafiya a yankin.
DSP Onyemaka Andrew wanda shine kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta ya shaidawa wakilin sashen Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa yanzu haka mutane biyu na hannun su sakamakon harin da aka kai a birnin Asaba dake jihar ta Delta.
Yace ko baya ga kame wadannan mutanen, yanzu haka rundunar tana nan tana ci gaba da bincike, dominzakulo masu hannu cikin wannan danyen aiki.
Ga Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani:
Facebook Forum