Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an gwamnatin Aljeriya sun ce Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya sami wani dan bugun zuciya


Shugaba Abdelaziz Bouteflika
Shugaba Abdelaziz Bouteflika

Jami’an gwamnatin Aljeriya sun ce Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya sami, abin da su ka kira, wani dan bugun zuciya, kuma ya na kan jinya a kasar Faransa.

Jami’an gwamnatin Aljeriya sun ce Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya sami, abin da su ka kira, wani dan bugun zuciya, kuma ya na kan jinya a kasar Faransa.

Firayim Minista Abdelmalik Sellal ya tabbatar da labarin jiya Asabar, tare da cewa halin da Shugaban ke ciki ba mai hadari ba ne. Ya ce Shugaban ya yi fama ne da ‘yar toshewar magudanar jini na wani dan lokaci a jiya Asabar kuma ya na kan murmurewa, kafin gwaje-gwajen da ke biye.

Mr. Bouteflika ya shugabanci Aljeriya tun 1999, kuma ana ganin ya na fama da rashin lafiya cikin ‘yan shekarun nan. Ba kasafai ya kan shiga jama’a ba.

Mr. Boutiflika ya kaddamar da sauye-sauyen siyasa cikin 2011, sanadiyyar wata gagarumar zanga-zangar jama’a, da ke da alaka da zaburowar juyin juya halin Larabawa.

Aljeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da su ka fi arziki, kuma daya ce daga cikin kasashen da su ka fi sayar ma Nahiyar Turai iskar gas.
Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG