Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagoran Juyin Mulkin Nijar Ya Maida Martani Kan Abubuwan Da Taron CEDEAO Ya Tsayar


ECOWAS
ECOWAS

Shugaban gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana matsayinsa dangane da sharudan da kungiyar CEDEAO ta gindaya a karshen taron da shugabaninta suka gudanar ranar lahadi, a cewarsa da dadewa Nijar ta cike ka’idodin da aka shimfida mata game da wannan dambarwa.

Da ya ke bayani a wata hira da aka watsa ta kafar talabijin mallakar gwamnati jim kadan bayan kammala taron shugabannin kasashen yammacin Afrika (CEDEAO), Janar Abdourahamane Tchiani ya tabo batun tsare hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa, inda ya ce ba a gidan kaso su ke tsare ba, suna cikin gidansa, kuma sun ba iyalinsa damar tafiya duk inda su ke so amma Bazoum ya ki, ya na mai cewa in dai ba tare da iyalinsa zai tafi ba, gwamma su zauna.

Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Shugaban majalisar CNSP na ganin sakin shugaba Bazoum a halin da ake ciki a yau a Nijar wani abu ne da ka iya zama babbar barazana.

Dangane da batun takunkumin da ECOWAS ta kakaba wa kasar da kuma irin sharudan da ta gindaya, shugaban gwamnatin mulkin sojan na ganin akwai wata manufar boye tattare da wannan lamari.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG