Gwamnatin Najeriya ta fara wayar da kan yara mata hade da kaddamar da shirin rarraba kayan tsabtar al'adarsu.
Rashin fahimtar ilmin tsabtar al'ada na daga cikin matsalolin da ka iya illata lafiyar ‘ya’ya mata a yayin da suka shiga wannan yanayi saboda yadda ake bukatar mace ta kasance cikin tsabta a lokacin.
Baya ga koke-koken masu fafutuka da dama a fadin Najeriya kan rashin kula da ilimin tsabtar al'adar ‘ya’ya mata, gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin ba da tallafin kayan tsabtar al'adar mata saboda a samu mafita kan matsalolin da suke fuskanta.
Yayin kaddamar da shirin, Ministan kula da al'amuran mata Pauline Tallen, ta ce wannan fanni na rayuwar mata na da matukar muhimmanci.
Tallen ta kuma yi kira ga al’uma da su shiga cikin lamarin taimakawa ‘ya’ya mata ta fanning samar da kayan tsabtar al'ada domin gwamnati kadai ba za ta iya ba sai da hadin gwiwarsu.
An dai kaddamar da tallafin ne saboda tsada, karancin kayayyaki tsabta da yanayin al’uma wajen ba da gudunmuwa ga mata da ‘ya’ya mata a lokacin bukata.
A wani bangare kuwa, Ambassada Rukayya Muhammad, mai rajin kare yara da matasa ta bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta fara gangamin wayar da kai ne kafin ta kaddamar da tallafin kayan tsabtar al'adar.
A nata bangare, jagorar cibiyar kula da tsabtar ruwa da ake rarrabawa, Ms. Elizabeth Jeiyol, ta bukaci masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe wajen taimakawa gwamnati domin kawo sauyi da ake bukata a wannan fannin.
Ministar harkokin da suka shafi matan dai ta kaddamar da tallafin ne a kauyen Kado da ke birnin Abuja a ranar da aka ware domin duba ci gaba da aka samu a fannin tsabtar al'adar mata tare da hadin gwiwar jagorar cibiyar kula da tsabtar ruwa da ake rarrabawa domin taimakawa mata a lokacin al'adarsu ta wata-wata.
Saurari karin bayani daga Halima Abdurra'uf a sauti:
Facebook Forum