Wasu hare-haren boma-bomai sun hallaka mutane 7, wasu kuma sun jikkata a babban birnin Jakarta na kasar Indonesiya. Kungiyar ISIS, da ke fafutikar kafa daular Islama ce ta dauki alhakin kai harin.
Harin Boma Bomai a Kasar Indonesiya
Sojoji sun kewaye wajen da aka kai hari a babban birnin Jakarta na kasar Indonesiya, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7.

5
'Yan sanda sun kewaye wani gini kusa da inda aka kai harin.

6
Sojojin Jakarta sun je wajen da aka kai harin.

7
Sojoji sun je wajen da aka kai harin da motocin yaki a birnin Jakarta.