Kananan hukumomin uku dai a yan kwanakin nan sun yi fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da rikicin makiyaya da manoma yan kabilar Bachama, lamarin da ya jawo asarar rayuka fiye da dari, kuma wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin nemo bakin zaren maido da kwanciyar hankali a yankunan.
Wannan gargadi dai ya biyo ne bayan wasu rahotanni dake cewa yayin da ake kokarin maido da zaman lafiya a yankunan da rikicin Fulani da al’umman Bachama ya shafa, yanzu haka akwai wasu kungiyoyi dake fakewa da sunan banga suna fidda mutane a mota suna kissan dauki dai dai, batun da gwamnati tace ba zata kyale ba.
Gwamnan jihar Adamawan Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, wanda ya nuna kaduwar gwamnatin jihar dangane da wannan sabon lamari, ya gargadi sarakunan yankin da su dakatar da wadannan kungiyoyi, ko kuma duk wanda aka kama ya gamu da fushin hukuma, komin matsayinsa.
Facebook Forum