Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar TETFUND Zata Sake Gina Dakin Karatun Jami'ar Jos da Gobara Ta Lakume


Dakin karatun jami'ar Jos da gobara ta lakume
Dakin karatun jami'ar Jos da gobara ta lakume

Gidauniyar dake tallafawa makarantun dake gaba da sakandare da ake kira TETFUND tayi alkawarin gyara dakin karatun Jami'ar Jos da gobara ta kone kurmus ba tare da barin komi ba a watan jiya.

Babban sakataren gidauniyar Dr Abdullahi Baffa shi ya bayyanawa manema labarai hakan yayinda ya kai ziyarar gani da ido a harabar jami'ar.

Dr Baffa ya bayyana takaicinsa kan irin barnar da wutar tayi a babban dakin karatun na jami'ar. Yace gobarar ta yi masu barna ba kadan ba. Duk littafan dake ciki da naurorin kwamfutoci dukansu suka kone. Ba'a ma batun kujeru da sauran kayayyakin dake ciki

Dakin karatun Jamai'ar Jos da gobara ta lakume
Dakin karatun Jamai'ar Jos da gobara ta lakume

Dr Baffa yace ba karamin tashin hankali ba ne a wurinsu, musamman ga hukumarsu wadda ta kasance itace take samarda tallafi domin bunkasa ilimi mai zurfi a kasar.

Dangane da tallafin da hukumar zata bayar, Dr Baffa yace mafi karancin abun da zasu yi shi ne "duk abun da ya kone mu dawo masu dashi", inji Dr Baffa. Duk abun da ya lalace zasu gyara. Zasu yi duk abun da zasu yi dakin karatun ya koma kamar ba'a yi gobara ba.

Shi ko shugaban jami'ar Farfasa Sebastine Maimako yace duk da yake ba zai iya bada adadin hasarar da aka yi a gobarar ba, amma sun bukaci manyan malaman jami'ar kowannensu ya bada miliyan guda guda yayinda sauran malamai da dalibai zasu bada tasu gudummawar.

Shugaban yace littafan ba suka kone sun kai dubu tamanin banda wadanda suke sassa daban daban.

Wasu daliban da aka zanta dasu sun bayyana irin matsalar da suka shiga wajen yin karatu sanadiyar gobarar.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG