Gwamnan Jihar Adamawa Bindo Jibrilla ya ce ficewar tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar daga jam'iyar APC mai mulki ba zai sa shi ma ya fita daga jam’iyar ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Aksarin jaridun Najeriya, sun karkata hankulansu kan ficewar Atiku daga jam’iyar ta APC a ‘yan kwanakin nan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Jibrilla yana cewa ficewar Atiku daga jam’iyar ba za ta shafi farin jininta a jihar ta Adamawa ba.
A cewar Jibrilla, Atiku ya kai minzalin da zai yankewa kansa kowace irin shawara a fannin siyasa kamar yadda jaridar ta wallafa.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Atiku ya bayyana ficawar shi daga APC bayan da ya zargi jam’iyar da karkata akalar tafiyarta.
Daga cikin batutuwan da ya bayyana, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce jam'iyar ba ta damawa da matasa.
Facebook Forum