Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faduwar Darajar Naira Ya Fara Shafar Kasuwanci A Nijar


Faduwar darajar Naira
Faduwar darajar Naira

Faduwar darajar Naira a Najeriya ya fara shafar wasu harkokin kasuwanci a makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar inda ma su harkokin kasuwanci ke cewa lamarin ya shafe su matuka.

Da yawa daga cikin kananan ‘yan kasuwa sun tabka asara mai yawa sakamakon fadiwar darajar kudin na naira.

Hakan ya fara kawo cikas cikin harkoki na ‘yan kasuwar Nijar da suke ma’amala da ita wannan naira domin saye da sayarwa a tarayyar Najeria, lamarin da ya sa al’amurran suke fuskantar koma baya ta fannoni da dama.

Matsalar fadiwar naira tafi shafar kananan ‘yan kasuwa kai tsaye inda wasu daga cikin kananan ‘yan kasuwar ke duba yiwuwar jingine kasuwancinsu har al’amurra su daidaita.

Masana tattalin arziki irin su Malam Aminou Ibrahin na jan hankalin ‘yan kasuwar da su samar da wani shirin da zasu tsira daga kariyar tattalin arziki, duba da irin tasirin da tarayyar Najeriya ke dashi a Nijar ta fuskar kasuwanci.

Sai dai yayinda yan kasuwar ke kokawa kan wannan matsalar, wasu kuma anfani suke yi da wannan damar domin zuwa sayen kayayyakin da ake samowa a tarayyar Nigeria.

A saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:

Fadiwar Darajar Naira Ya Fara Shafar Kasuwanci A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG