Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ta Fara Binciken Masu Dora Labaran Karya A Kan Zaben Amurka


Facebook
Facebook

Ana ci gaba da yunkurin cusawa masu kada kuri’a zaben Amurka na tsakiyar wa’adi da za a gudanar a watan Nuwamba ra'ayi, koda yake kamfanoni masu zaman kansu da jami’an gwamnati suna dari darin bayyana takamanman wanda aka gano yana aikata hakan.

Kamfanin Facebook ya sanar a jiya Talata cewa, ya rufe shafuka 32 na Facbook da Instagram saboda an samu suna da hannu a aikata ba daidai ba.

Facebook ya fada a wani sakon da ya buga cewa, yanzu ne aka fara bincike don haka ba a gama tattara bayanai ba, da ya hada da ainihin wanda ya shirya wannan abu. Babban kamfanin sada zumuntan yace duk wanda ya bude wannan shafin ya wuce gona da iri har ma ya bad da kamanni fiye da yanda wata cibiyar yanar gizon Rasha ta Internet Research Agency (IRA) ta yi a baya.

Wani mai fashin baki Micheal Posner, yace Facebook na bukatar wani sashe da zai kula da ayyukan Rasha

Yace Facebook da Google sun fada mana cewa basu bukatar wani dan Rasha ko kuma wani rukunin yan Rasha da zasu kula da barazanar Rasha a matsayin wata babbar matsala ta labaran karya. Kuma bamu amince da hakan ba. Abin da Rasha ke yi wata babbar barazana ce ga demokaradiyar mu, don haka Facebook da Google da Twitter suna bukatar wani rukunin yan Rasha masu gaskiya su magance wannan matsalar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG