Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyar Kwallon Kafa: Wasannin Karshen Mako


Karawar Ajax da Bayern Munich a gasar UEFA
Karawar Ajax da Bayern Munich a gasar UEFA

A fagen tamaula, wasannin da za a buga a karshen makon nan sun hada da gasar La Liga sinda za a kara tsakanin Sevilla da Levante, sannan Athletico Madrid ta fafata da Getafe.

Baya ga haka, Girona za ta karbi bakuncin Barcelona a ranar Lahadi.

A gasar Bundesliga ta Jamus kuma, Mainz za ta kara da Nurnburg ne yayin da Dortmund za ta kara da Hannover, sannan Wolfesburg ta gwada kaiminta da Bayer.

A gasar Seria A kuma ta Italiya, Milan za ta karbi bakuncin Napoli sai kuma Chievo ta kara da Fiorentina.

A can kasar Faransa kuwa ta Ligue 1, Dijon FCO za ta karbi bakuncin Monaco a gobe Asabar kana a ranar Lahadi Montpellier ta kara da Caen.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG