Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dogayen Layukan Fetur Sun Dawo A Babban Birnin Najeriya Abuja


Layin neman Mai
Layin neman Mai

An wuni da dogayen layukan masu neman man fetur a babban birnin Najeriya Abuja inda maasu motoci ke yin layuka da kan kai ga datse tituna.

Duk gidajen man da ke tsakiyar birnin na cike da motoci inda masu sayar da man a jarka ke sayarwa kan farashi mai tsadar gaske.

masu sayar da mai a jarakuna
masu sayar da mai a jarakuna

Baya ga bayanan da a ka samu a kwanakin baya daga shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kolo Kyari cewa akwai wadataccen man, ba wani bayani na dalilin wannan karancin man.

Akwai ma rade-radin da ke nuna wasu gidajen man sun kara farsahin litar mai biyo bayan batun kara farashin man ta bayan gida.

Gidan man da Muryar Amurka ta ziyarta a AREA 3 na da dogon layi amma bai kara farashin ba da ya wuce sauyawa daga Naira 162 zuwa 165.

Tun janye batun karin farashin litar fetur a farkon watan nan a ke ta samun cikas wajen wadatar man, kazalika an samu matsalar kawo mai mai illa da ya haddasa samun matsala ga motoci.

Kamfanin NNPC ya bayyana cewa man na dauke da wani sinadari ne na “methanol” da ya wuce kimar da Najeriya ke amfani da shi.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG