Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ɗabi'ar Shan Minti Tsakanin Samari Da 'Yan Mata


Wata sabuwar dabi'a da matasa maza da mata suka kirkiro kuma suke ganin tamkar burgewa ce ita ce dabi'ar shan minti!

Shan minti kamar yadda matasan da muka tattauna da su suka bayyana wata hanya ce da samari ke anfani da ita domin yi ma 'yan mata dabara domin samun damar kwatanta rayuwar tsuntsaye da su watau kiss.

Baya ga kiss ko shan minti, akwai sauran dabi'u irin su yin rakiya da kuma shan ice cream wanda samarin suka kwatanta a matsayin wata dabara da samarin da 'yan mata kan yi anfani da ita domin tafiya nesa inda ba'a san su domin aikata wasu abubuwa da basu dace ba.

'Yan mata dai kan yi ma iyayensu karyar zuwa bikin kawayen su ko kuma wani abu makamancin haka domin samun biyan bukatun kan su.

ku saurari cikakkiyar hirar, kuna iya sauraren mu kai tsaye ta yanar gizo a wayar ku ta salula ta www.dandalinvoa.com.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG