Malam Aminu Dambazau kwararren malami ne a fannin Zamantakewa da ci gaban al'uma a jami'ar Bayero dake Kano a Najeriya, kuma ya yi mana karin bayani akan auren dole da kuma matsalolinda ke tattre da auren dole.
Kamar yadda ka sani, kudi babu abin da baza su iya sa wasu mutane suyi ba, har bautamaka sai su yi ida kana da kudi. Dan haka kwadayin abin duniya na daya daga cikin dalilan da suke ingiza wasu iyaye yi ma 'ya'yan su auren dole.
Dalili na biye kuma shine jahilci, malamin ya kara da cewa lallai jahilci yana taka rawar gani a wajan sa yi ma 'ya'ya auren dole. malamin ya ce idan mautane nada ilimin addini da na boko, za su ga cewar akwai iya mizanin karfin da iyaye ke da shi akan 'ya'yan su, dan haka bai kamata iyaye su cika takurawa 'ya'yan su ba har ma daga karshe su yi masu auren dole.
A kwai kuma matsalolin auren zumunci da yawancin jama'a ke sa 'ya'yan su ciki domin a nasu ganin, duk 'yan uwa dan haka babu matsala amma ba haka zancen yake ba.
Saurari Cikakken Bayanin.