Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Zabi Okowa A Matsayin Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa A PDP


Gwamna Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)
Gwamna Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)

Kafin ya zama gwamna, Okowa Sanata ne a majalisar Dattawan Najeriya inda ya wakilci arewacin jihar Delta karkashin jam’iyyar ta PDP.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi A. Okowa a matsayin abokin da zai taya shi takara.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis yana mai nuna farin cikinsa da zabin Okowa.

“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Gwamna Ifeanyi A. Okowa ne abokin takarata.” Atiku ya ce.

Hukumar zabe ta INEC ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasar kasar nan da ranar 17 ga watan Yuni, a matsayin wa’adi da za su gabatar da dukkan ‘yan takararsu na mukamai daban-daban da mataimakansu.

Sa’o’i kafin cikar wa’adin, jam’iyyar ta PDP ta kafa wani kwamiti mai dauke da mambobi 17 don tantance Okowa a ranar Alhamis.

Dan shekara 63, Okowa na wa’adin mulkinsa na gwamna na karshe a jihar ta Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Kafin ya zama gwamna, Okowa Sanata ne a majalisar Dattawan Najeriya inda ya wakilci arewacin jihar Delta karkashin jam’iyyar ta PDP.

Asalinsa dan kabilar Ika ne daga yankin Owa-Alero da ke jihar ta Delta mai arzikin mai.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

Atiku Ya Zabi Okowa A Matsayin Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa A PDP - 2'46
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG