WASHINGTON D.C. —
An soma bayyana karfin gwiwar cewa watakila za’a sami wani gagarumin ci gaba a kokarin da ake na cimma yarjejeniyar sulhu a tsakanin Amurka da wakilan kungiyar mayakan Taliban na Afghanistan da ke taro a Qatar.
Ana fatan wannan taro zai iya kawo karshen yakin da aka share shekaru 17 ana yi a kasar ta Afghanistan.
Tun a ranar Litinin aka soma wannan taron, inda wakilan Amurka ke karkashin jagorancin wakilin Amurka akan Afghanistan din, Zalmay Khalilzad, tare kuma da wakilicin jami’an kasashen Pakistan da Qatar.
Yayin da aka shiga rana ta 4 da soma taron ne, wasu kafofi suke fadawa gidan rediyon nan na Muryar Amurka cewa, sassan biyu na samun gagarumin ci gaba a kokarin da suke na cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa.
Facebook Forum