Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zartar Mata Da Hukuncin Kisa Ta Amfani Da Allurar Dafi


An kashe wata mata da aka tuhuma da aikata laifin kisan mijinta a shekarar aluf dari tara da tasa'in da bakwai a jihar Georgia dake kudu maso gabashin Amurka, duk da kokarin da aka yi wajen kauce wa hukuncin kisan da kuma rokon da Paparoma Francis yayi na kada a hallaka matar.

Ms. Kelly Gissendaner ta mutu a safiyar yau laraba ta hanyar yi mata alurar dafi a gidan kason dake wajen Atlanata, babban birnin kasar. Ita dai Ms. Gessendaner ‘yar shekaru 47 da haihuwa, ita ce ta kasance mace ta farko da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar.

Da da farko an shirya kashe Ms. Gissendaner a daren jiya Talata, amma aka jinkirta shirin don lauyoyinta sun bukaci kotun jihar da na tarayya da su dage kisan amma abin ya ci tura, ciki harda neman dage kisan har sau uku da suka yi ga kotun kolin Amurka.

Archbishop Carlo Maria Vigano, shi ne wakilin diplomasiyyar Paparoma Francis, ya tura wa hukumar yin afuwa wasika a madadin Paparoma, inda ya nemi hukumar ta sassauta hukuncin kisan zuwa wanda zai nuna adalci da jinkai. Ita wannan hukumar dai itace kadai ke da ikon yin afuwa a jihar Georgia.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG