Kamar yadda mujallar The Punch ta wallafa, Kusan 'yan Hursuna talatin da biyar ne wata kotu dake karkashin jagorancin mai shari'a Hamidu Kunaza a jahar Bauchi ta yi ma afuwa ranar talatar da ta gabata.
A cewar mai magana da yawun jami'an tsaron gidan yari na jahar Bauchi Adam Jibrin, an saki 'yan gidan hursunan ne a sanidiyyar kokarin rage cunkoson 'yan gidan hursunan bayan sake biyawa kan iin laifukan da suka aikata wanda ya yi sanadiyyar kai su ga gidan kasson.
Jibrin ya bayyana cewar wadanda aka saki yawancin su wadanda suke tsare ne a gidan yarin har na lokaci mai tsawo ba tare da anyi masu shari'a ba.
Mai shari'ar ya bayyana cewa yana taya mutanen murnar samun wannan dama, kuma ya yi kira gare su baki daya da su kasance masu natsuwa da kuma anfani da wannan damar domin sake sabuwar rayuwa.
aga karshe ya gargade su da su zama masu kaucewa duk wani irin laifi da zai sa rauywar su cikin ayyukan da na sani, ko kuma abinda zai sake mayar da su cikin gidan hursuna.