An kama masu zanga-zangar sanye da rigunan Dole Buhari ya tafi ko kuma "Buhari Must Go" a turance ne a lokacin da suke gudanar da ibada a Dunamis International Gospel Centre, wata fitattar coci a babban birnin tarayya Abuja. Amma kungiyar kare hakkin dan adam din ta ce kamewar da kungiyar leken asirin ta yi ba bisa ka'ida ba ne kuma cin fuska ne ga kundin tsarin mulki.
Lauyoyin masu zanga-zangar da aka tsare sun kalubalanci kame su a kotu cewa an take musu hakkokinsu na asali. Suna kuma neman kusan $ 24,390 ga kowannensu don abin da suka ce ci gaba da tsare su ba bisa doka ba.
Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, Muryar Amurka, zanga-zangar, Nigeria, da Najeriya.
Deji Adeyanju shi ne wanda ya jagoranci kungiyar ta kare hakkin bil adam da kuma bin doka da oda, ya kuma fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa dole ne gwamnati ta saki masu zanga-zangar nan take ba tare da wani sharadi ba. Ya kuma kara da cewa ba abu ne da za a yarda da shi ba ga gwamnati ta sanya laifi ga zanga-zangar, wacce kundin tsarin mulkin kasar ya kare.