WASHINGTON, DC —
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA,, ta cafke wani mutun dan shekaru 34, da katin Banki na ATM, guda 108, na Bankuna daban daban a tashar jirgin sama na Murtala Muhammad dake Lagos.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Ofoyeju Mitchell, ya ce an cafke mutumin ne akan hanyar sa ta zuwa kasar China dauke da katunan da sunayen mutane daban daban.
Katunan sun kunshi na Banki FCMB, guda 58, na Bankin Stanbic23, Bankin Zenith, 19, Bankin Fidelity 6, da Bankin Diamond guda 2.
Mrs. Victiria Egbase, Daraktan kadarori da abubuwan da suka shafi kudade na NDLEA, ta ce bayan da hukumar ta tabbatar laifin ta mika shi ga hukumar EFCC.