An kama wani gawurtaccen mai satar mutane mai suna Henry Chibueze, wanda aka fi sani da Vampire, tare da mai taimaka masa da bayanai.
Jami’an tsaro sun cafke shi ne akan hanyarsa ta zuwa sace wani alkali a masaukinsa dake kan titin Onitsha zuwa Owerri.
Chibueze, ya fadawa jami’an tsaro cewa yana gudanar da aiyukan sace mutane a sassa daban daban na Najeriya, Jamhuriyar Benin da kuma kasar Abidjan, inda matarsa da ‘ya’yan sa suke, ko da yake yace matar sa ta dauka shi dan kasuwane mai sana’ar saye da sayar da kayayyakin sawa.
Yace yana da wani Soja dan leken asiri wanda ya kuma kasance dan kungiyar Boko Haram, mai suna Hakeem Bello, daga jahar Kwara.
Ya kara da cewa yana da wata budurwa a Legas, wacce ta gudun masa da kudi Naira Miliya 45, wanda hakan ya sa ya kashe ta da iyayenta.
An kama bokan sa Alexander Ohigide, da mai yi masa ajiyar kudi, haka shi ma Hakeem, Sojan dake yi masa leken asiri ya shiga hannu.