Wani rahoto da ya fito daga ofishin 'yan sandan jahar Zamfara ya bayyana yadda wani jami'an suka yi awon gaba da wani matashi mai suna Yusuf Saleh mai shekaru goma sha biyar a yayin da ya yi kokarin kutsawa cikin dakin kwanan daliban makarantar gaba da sakandire (FCET) dake babban birnin jahar.
Kamar yadda mujallar Daily Trust ta walla, matashin ya shiga dakin 'yan matan ne a misalin karfe shidda na yamma 6pm, inda yayi shiga irin ta mata domin ya rika leka 'yan matan a lokacin da suke wanka ko suke tsirara.
Gano matashin a cikin harabar makarantar ya jefa daukacin makarantar cikin rudani a lokacin da daliban suka yi tsammanin ko matashin dan kungiyar boko haram ne ya je da niyyar kai masu hari.
A cewar shugar daliban makarantar Maryam Ibrahim, anga matashin sanye da hijabi, kuma ya daura kallabi kuma sa'annan daure da zane tamkar 'yar budurwa.
Maryam ta kara da cewar, kawarta wadda ta gano cewar namijine ba mace ba ita ta janyo hankalin sauran daliban, yayin da suka yi maza maza suka cafke shi suka kuma hanunta shi ga jami'an tsaron makarantar.
A cewar matashin, ya yi shigar ne domin samun damar shiga cikin makarantar sannan kuma yana so yaga yadda wurin kwanan daliban yake.