Ma’aikatar shariar Amurka, ta tuhumi Julian Assange, mutumin da ya kafa dandalin kwarmata bayanai ta hanyar sadarwar internet wato WikiLeaks, da laifin hada baki, wajen yin kutsen, na’urar kwamfuta, inda ta zarge shi, da taimakawa tsohon jami’in sojan ayyukan leken asiri, Chalsea Manning, da fallasa bayanan sirri.
A cikin tuhumar, an bayyana cewa, a watan Maris na shekara ta dubu biyu da goma, Assange ya hada baki, da Chalsea Manning, suka saci hanyar kutsawa rumbun kwamfuta, da ake ajiye bayyanan sirri, na gwamnatin Amurka.
Wannan sanarwar, ta zo ne, ‘yan sa’oi, bayanda, Birtaniya, ta kama Assange, yau alhamis, wannan shine mataki na baya-bayan da aka dauka da ya shafi harkokin shari’a na tsawon shekaru bakwai.
Assange, ya fake, a ofishin jakadancin Ecuador, tun shekara ta dubu biyu da goma sha biyu, domin gudun kada a tasa keyarsa, zuwa Sweden inda ake tuhumar sa, da laifin fyade.
Daga baya, Sweden ta janye tuhumar da take yi mashi, amma, ya ci gaba da zama a ofishin jakadancin, domin gudun kada Birtaniya, ta tasa keyar shi zuwa Amurka dangane da bayanan sirrin gwamnati, da dandalin WikiLeaks da ya wallafa.
Facebook Forum