Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al-Mustafa ya jagoranci yan Arewa da kabilar Igbo suka kaiwa Farfesa Ango Abdullahi ziyara.


Maj. Hamza Al-Mustapha a wani hoto da aka dauka a 2012.
Maj. Hamza Al-Mustapha a wani hoto da aka dauka a 2012.

Manjo Hamza Al-Mustafa yace sun kawo shugababnnin na Igbo ne saboda a fahimci juna da ‘yan kabilar Igbo.

Major Hamza Al-Mustafa yace sun kawo shugababnnin na Igbo ne saboda Farfesan ya sa baki a cikin lamari kuma doin a fahimci juna da ‘yan kabilar Igbo. Sa’anan kuma idan ya ji bayanin su Igbon sai ya gayawa yan uwansa yayen mu na bangaren Arewa don su san cewar wannan magana ta mutu, su yiwa gwamnoni da sarakuna da manya na Arewa gaba daya bayani.

Major Al-Mustafa yace tun fil azal an an fahimtar da mu cewar Najeriya itace a gaban mu. Tun ina da anini daya na yi yaki, wasu kasashe da suka sha fama da yake yake kamar Liberia,da Gambia, da Saliyo duk na je, kuma na je harda kasar Chad na je yankin Bakasi kuma duk wani rikici a Najriya daga 1983 babu wanda bani a ciki sai dai wanda aka yi shi ina gidan yari.

Don haka duk wanda ka ga yana neman rikici bai san rikici bane , to shi yasa muke so kasar nan ta zauna lafiya.

Major Al-Mustafa yace sun yi kira a waurin taro da suka yi cewa gwamnan jihar Kaduna ya saki matasan Arewa da aka kama kuma ya janye wannan doka ta kama su, kuma bama huruminta kwata kwata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG