Tsohon kocin ‘yan wasan Najeriya, Ladan Bosso, ya nuna kwarin gwiwar cewa Najeriyar za ta doke takwararta ta Mexico a wasan kusa da na karshe ko kuma Semi-final da za a buga a gasar cin kofin duniya a matakin ‘yan kasa da shekaru 17 da ake yi a kasar Chile .
‘Yan wasan Golden Eaglets sun lallasa Brazil ne a wasan quarter-final da ci 3-0, wanda hakan ya basu damar shiga rukunin kasashe hudu da suka rage a gasar.
Ita dai Mexico ta doke Ecuardor ne da ci 2-0.
Sai dai Bosso wanda ya jagoranci tawagar ‘yan wasan Najeriya a matakin ‘yan kasa da sheakru 20, ya yi gargadin cewa kada ‘yan wasan su sauya irin da’ar wasan da aka koya musu yayin da suke kokarin sake lashe kofin.
A cewarsa, idan har suka tsaya akan wannan horo, zai yi wuya sauran abokanan karawarsu su yi nasara a kansu.
Bosso ya kuma yaba da irin rawar da Victor Osimhen ke takawa wajen zira kwallaye inda ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar zai taimakawa Najeriya ta lashe kofin.
A gobe Alhamis ake za ran Najeriyar za ta kara da Mexico a filin wasa na Francisco Sanchez da ke Rumoroso a Chile.