Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar An Kammala Dukkan Shirye-Shirye Domin Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu.


Hedikwatar Hukumar Zaben Nijar CENI
Hedikwatar Hukumar Zaben Nijar CENI

Sai dai 'yan hamayya a kasar suna ci gaba da kiran magoya bayansu su kauracewa zaben.

Hukumar zabe ta jamhuriyar Nijar CENI, ta tabbatar da cewa ta kammala dukkan shirye shirye domin gudanar zaben fidda gwamnai da za'a yi Lahadi,20 ga watan Maris.

Zaben da za'a yi tsakanin shugaban kasa mai ci ne Muhammadu Isouffe, da kuma madugun 'yan hamayya,kuma tsohon kakakin majalisa Hamma Amadou, wanda ahalin yanzu aka kai shi kasashen wajen domin jinya. Kamin haka dai Hamma yana gidan kaso, inda hukumomin kasar suka tsare shi kan zargin fasakorin jarirai.

Amma 'yan hamayya suna kan bakarsu na ci gaba da kiran magoya bayansu su kauracewa wannan zabe, domin suna zargin an tafka magudi tun a zagaye na farko, kuma ba'a yi musu adalci ba da suka daukaka kara zuwa kotun tsarin mulkin kasar.

Haka nan sun kawo batun ci gaba da tsare dan takararsu Hamma Amadou.

Ibrahim Ka'almaseeh Garba ya aiko da wannan rahoto.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG