A daidai lokacin da Kurdawa ke tsallen murnar nasarar da suka samu na kuri’ar da mutanensu suka jefa na amincewa da su kafa yankin kansu mai cin gashin kansa, hukumomin Iraq din su kuma sun tashi haikan wajen daukan matakan horad da Kurdawan kan wannan kuri’ar tasu.
Daya daga cikin matakan farko da gwamnatin Iraq ta dauka shine rufe sararin samaniyar yankin don hana wa duk wasu jiragen sama shiga wurin.
Haka kuma Iraq tace zata hade kai da kasar Turkiyya don gudanarda atisayen sojojinsu na hadin-gwiwa.
A jiya Laraba ne kuma Majalisar Dokokin Iraq, wacce tace kuri’ar da Kurdawan suka jefa ta sabawa Kundin tsarin mulki, suka umurci Pr.ministan Iraq, Haider al-Abadi, da ya aika rundunonin soja zuwa lardin Kurdawan na Kirkuk mai arzikin man fetur don su kwace dukkan rijiyoyin man fetur dake yankin.
Bayan duka wannan, Majalisar Dokokin ta Iraq ta nemi kasashe 34 dake da opishin jakadanci a can Kurdistan da cewa su rufe ma’aikatun, sannan kuma a sauke gwamnan jihar Najmaldin Karim daga kujerarsa ta mulki saboda wannan kuri’ar da ya bari aka jefa.
Facebook Forum