WASHINGTON D.C —
A Janhuriyar Nijar daruruwan 'yan kasar ne suka tarbi sabon Zakaren wasan Taekwondo na Duniya Abdurazak Issoufou Alfaga kuma na kasar a gasar Teakwondo ta Duniya da aka gudanar a makon da ya gabata a kasar Koriya ta Kudu.
Matashin ya lashe babbar lambar wasanne sakamakon nirin kwazon da ya nuna a wajan wannan gasa, lamarin da jama'a da dama suke ganin zai karfafawa matasa da dama a jamhuriyar Nijer, da kuma sauran kasashen Afirka gwiwa.
Domin cikakken bayani ga rahoton da Yousoufou Aduloye ya aiko mana.
Facebook Forum