Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Dole Matasa Su Dogara Kacokan Kan Gwamnati Ba -Inji Samira Umar Dan kura


Samira Umar Dan kura
Samira Umar Dan kura

Ina da ilimin koyar da karatun kwamputa tun daga tunshe, tare da sarrafata kuma abinda da neke koyawa matasa a yanzu haka kenan inji Samira Umar Dan kura.

Samira ta ce, babban burinta a rayuwa bai wuce ta tara matasa tare da koya masu muhimmancin zama masu dogaro da kai, wato ba sai sun jira ko dogara da aikin gwamnati ba.

Matashiyar ta kara da cewa, duk da nisan karatun da take da shi ta fi sha’awar sana’ar aikin dogaro da kai kamar yadda ta ke yi a yanzu.

Samira, bayyana cewa tana da digiri na farko, sannan ta koma karatun gaba da digiri daga bisani ta samu digirin ta na biyu, inda ta ke cewa lokaci yayi da matasa zasu san cewa ba dole ne su jira gwamnati ta yi wa alumma komai ba.

Daga karshe ta kara da cewa baya ga gwamanti ba lailai ne matasa su dogara kacokan akan iyaye da ‘yan uwan da suka yi nisa a ayyukan gwamnati ba, su tashi su tsaye da kafafun su domin amfanin rayuwarsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:47 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG