WASHINGTON D.C —
Jami’an lafiya sun fitar da matashi me shekaru 38 da haihuwa dan kasar Mexico, me nauyin kilogiram 500, wanda ya kwashe shekaru shidda akan gadonsa daga gida zuwa asibiti domin bashi magani.
Mai Magana da yawun liktan ta bayyana cewa an dauki matashin zuwa asibitin Guadalajara, inda aka dauki jininsa domin yin wasu gwaje gwaje, ta kuma kara da cewa zai dauki lokaci mai tsawo yana karbar magani. Ana bukatar kayan aiki na musamman domin canza masa wuri.
Wani dan kasar Mexico mai suna Manuel Uribe, wanda ya rasu a shekarar 2014, ya fi kowa nauyi a duniya, ya rasu ne yana da shekaru 48, mai nauyin kilogiram 560, wanda sunansa ya shiga cikin littafin tarihi a matsayin wanda ya fi kowa kiba da nauyi a duniya.