Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Na Duniya


Dan wasan kasar Faransa mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid Antoine Griezmann, ya ce baya da sha'awar koma kungiyar PSG, Griezmann dai yana cikin Shahararun ‘yan kwallon kafa a yankin nahiyar turai, ya kuma fafata wasani a laliga na kasar Spain tun shekara 2014, Wanda a yanzu haka kungiyar PSG ke zawarcinsa.

Shima dan wasan kasar Brazil Casemir ya baiyana ra'ayinsa nakin komawa kungiyar Barcelona.
Casemir ya ce shi masoyin Real Madrid, ne don haka ba zai iya komawa Barcelona ba saboda wannan dalilin.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tace bata da niyyar sayar da dan wasanta mai suna Andreas Cristensen wanda ake rade radin cewa Barcelona na zawarcin sa.

Itama Manchester United ta nuna bukatar ta na zawarcin dan wasan tsakiya na Valencia mai suna Fran Villalba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00

XS
SM
MD
LG