Hukumomi a yankin gabashin kasar China, na kara zurfafa bincike wajen ganin an kamo sauran macizan da suka gudu, daga wani haramtaccen gidan kiwon macizan. Kimanin sama da macizan “Cobra” da turanci “Gamsheka” da hausa, dari biyu 200, ne suka gudu.
A watan Augusta da ya gabata ne, wasu ‘ya’ya macizan a wani gidan gona a yankin Nanjing a kasar china, suka gudu, hukumomi sun yi kokarin kama macizai sama da dari da hamsin 150, wanda suke kokarin kama saura fiye da hamsin 50.
Macizan dai nada tsawon inci bakwai 7, a cewar mai magana da yawun hukumomi a karamar hukumar Liuhe, Mr. Xinhua. Wanda ya kara da bayyanar da cewar, ana amfani da wadannan macizan ne wajen yin maganin gargajiya. Duk dai da cewar su wadannan jariran macizan, basu dauke da guba irin ta manyan gamsheka.
Sun kara da cewar, a watan Augustan dai an kai kimanin sama da kwayayen macizan dubu daya da dari takwas da ashirin 1,820 wannan gidan gonan, wanda aka kyan-kyashe kimanin dubu daya da dari biyar 1,500. Hukumomin basu da wata masaniyar hakan, har sai lokacin da mazauna kauyukan suka fara kashe macizan, amma suka ga basu karewa, sannan aka gano wannan aika-aikan da wasu mutane sukayi.