Wasu daga cikin jami’an hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, sun isa birnin Ndola, na kasar Zambia, kafin fafatawar da za’a yi ta wasan shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za’a buga a shekarar 2018 tsakanin Najeriya da kasar ta Zambia.
Jami’an da suka fara yin gaba sun tafi ne a karkashin jagorancin Mr Bola Oyeyode, mai kula da harkokin wassani a karkashin hukumar kwallon kafa ta Najeriya, domin tabbatar da shirya masaukan ‘yan wasan sa zasu bar Najeriya ranar Asabar idan Allah ya kaimu.
‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa na kungiyar Super eagles zasu tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport tare da sauran manya manyan jami’ar hukumar kwallon kafa ta Najeriya, da na ma’aikatar matasa da wasanni da wasu daga cikin ‘yan majalisar kasar da kuma manema labarai.
Mataimakin shugaban humar kwallon kafa ta Najeriya mataki na biyu Shehu Dikko , ya bayyana cewa sun riga sun ba wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin wasannin kwallon kafa kujerar zuwa kasar ta Zambia, domin anyi hayar jirginne domin ‘yan wasan kungiyar ta Super Eagles, kuma sai kowane dan wasa ya sami kujera kafin kowa ya samu, a cewar mataimakin shugaban.
Ya kara da cewa “bamu da isassun kudade dan haka yawancin wadanda zasu bi tawagar domin goya masu baya kuma mun fada mun fada masu bamu da kudin daukar nauyin su, dan haka kowa zai dauki dawainiyar tafiyarsa da kuma wurin kwanansa kuma duka sun amince”, a cewar Shehu Dikko.