Kana ko kina kusantar shekaru 25 da haihuwa, kuma kun kammala karatun jami’a, kun fara aiki? Ga wasu kadan daga cikin abubuwa da kan iya taimaka ma rayuwar ku ta inganta. Wadane irin baiwa Allah, yayi maka na amfani da basirar ka, kodai wajen zane ko iya sarrafa wasu abubuwa da zasu iya kawo maka kudin shiga koda baka aiki? Kokarta gyaran jiki, da wajen zama ko kwanciya, haka kada ku shiga soyayya wadda kan iya haifar da damuwa a tsakanin ku idan baku shirya yin aure ba.
Kana kokarta wajen tambayar abun da baka sani ba kodai a wajen aiki ko a cikin abokai da kawaye, batare da jin kunya ba. A kokarta karance karancen littattafai da suka hada da ilimin rayuwa da ma labaran wasu magabata da suka zama wani abu a rayuwar su, tsara yadda mutun ke kashe kudi shima wani abune da kan iya taimakon mutun cimma burin shi a rayuwa. Haka samu lokaci don rayuwar kadaici, wanda zaka iya tunani ko tsara wasu abubuwa da kan amfane ka da wasu.
Bama kai karfin gwiwa wajen kokarin aiwatar da wani abu da ke da wuya, muassamman abun da kaga wasu sunyi amma sun wahala. Kokarta wajen ganin kaci abun da zai gina maka jiki da baka lafiya, haka nesanci duk wani abu da lafiyar jikin ka bata bukata. Daukan hutun awa daya a wajen aiki nada matukar muhimanci ga rayuwar mutun. Kokarta nesanta kanka da abokan da basu da amfani gare ka ko ga wani naka, musamman ma a shafufukan yanar gizo. Duk wani aboki da baka karuwa da shi a shafin ka, hanzarta goge shi ko ita. A karshe kokarta zama mutumin da baya tsoron duk wani abu da yake sabo a rayuwar shi, kuma zama mutun mai gaskiya a kowane hali ka samu kanka, sai kokari wajen magance duk matsaloli da suka kusanto ka batare da ka shiga hanyar wani ba.