A ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2014, ne wani jirgi kirar MH370 Boeing 777 mai dauke da mutane 239, na kasar Malaysia, ya bace jim kadan bayan tasowar shi daga babban birnin Kuala Lumpur zuwa Beijing a kasar China.
A cewar gidan talabijin na CNN, wani ba’amurke dan yawon shakatawa mai suna Blaine Gibson, ya bayyanar da wani fallen karfe da yace yana kyautata zaton bangaren jirgin kasar Malaysia ne da ya bace kimanin shekaru 2 da suka wuce. Wannan fallen ya kai kimanin tsawon mita daya, da fadin taku 4. Abun dubawa a nan shine, an dai ta neman wannan jirgin da mutane dake ciki a tekun Indian ocean, amma sai kuma anga wani bangaren shi a yankin kasashen Afrika.
Ya dai tsinci wannan bangaren jirgin ne, a wani daji na kasar Mozambique, a dai-dai lokacin da yake wani yawon shakatawa a yankin. Yanzu dai haka an aika da wannan karfen zuwa kasar Australia don tantance gaskiyar wannan karfen.