Abun mamaki baya karewa, a satin da ya gabata ne wata yarinya Taylor Gammel, mai shekaru 19, ta bata na tsawon awowi. Taykor, ta tashi cikin dare ta fita daga gidan su, cikin magagin bacci tayi ta tafiya wanda har takai kimanin tafiyar kilomita goma sha hudu 14.
Iyayen yarinyar sun kira ‘yan sanda da misalign karfe shida 6, na asuba don sanar dasu cewar basu ga ‘yar suba. An bazama neman ta sai aka tsince ta a cikin gari kusa da gidan kawun ta, tana tafiya. Ta bayyanar da cewar bata iya tuna komai tun barin ta gidan su, sai kusan yanzu da takai wajen gidan kawun nata.
Ta kara dacewar abunda yasa ma ta iyagane cewar tana cikin wani hali, shine yadda kafafunta suka fara yimata zafi, domin kuwa bata sanye da takalmi a kafarta, tana kuma sanye ne da kayan bacci a jikinta. A cewar wani likita Dr. Shlini Paruthi, abun da ya faru da wannan yarinyar bawai bakon abu bane, hakan na faruwa da mutane da dama, har ma su shiga wani yanayi na daban. Wannan shine ake cema dimuwa cikin bacci. Likitan ya kara da cewar akasarin yara daga shekaru biyar 5 zuwa ashrin 20 yara kan samu wannan matsalar, amma abun yi a nan shine iyaye su dinga kula da yara da kuma gudun ajiye wasu abubuwa da ka iya ji musu ciwo.