Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Amince Da Takardun Mutane 7 Akan Shugabancin Hukumar


Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta amince da takardun tsayawa takarar mutane 7 masu son maye gurbin Joseph Blatter a matsayin shugaban FIFA a lokacin babban taro na musamman da zata yi a shekara mai zuwa, sai dai kuma sunayen ‘yan takarar bai hada da na wani tsohon dan wasa mai suna David Nakhid ba.

Wata sanarwar da hukumar FIFA ta bayar a shafinta na intanet yau laraba ba ta bayyana dalilin kin karbar takardar takarar Nakhid, wani tsohon dan wasan kasar Trinidad da Tobago ba, amma ta ce hukumomin kwallon kafar kasashen duniya sun gabatar da sunayen ‘yan takara 7.

Jiya talata, ranar karshe ta mika takardar neman tsayawa takara, sakatare janar na hukumar kwallon kafa ta kasashen Turai, UEFA, Gianni Infantino, da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Liberiyha, Musa Bility, da kuma wani dan gidan sarautar kasar Bhrain mai suna Sheikh Salman bin Ibrahim al Khalifa, sun bayyana cewar suna daga cikin wadanda suka mika takardun tsayawa takara.

Sauran wadanda ke takarar sune shugaban hukumar kwallon kafar Turai, UEFa, Michel Platini, da Yarima Ali bin al Hussein na kasar Jordan, da wani dan kasuwa dan kasar Afirka ta Kudu Tokyo Sexwale wanda aka daure a kurkuku lokacin mulkin wariyar launin fata da kuma wani tsohon jami’in hukumar FIFA, Jerome Champagne.

Platini shine ke kan gaba cikin wadanda ake sa ma ran lashe wannan kujera kafin hukumar kula da da’a ta FIFA ta dakatar da shin a tsawon kwanaki 90 tare da shugaba mai ci Blatter, yayin da ake binciken wani kudi kimanin dala miliyan 2 da hukumar FIFA ta biya shi tsohon dan wasan na Faransa a shekarar 2011.

A saboda wannan dakatarwa, kwamitin kula da zabe na FIFA ba zai tace sunan Platini a yanzu ba, har sai bayan wannan dakatarwa ta kare ko an dage ta kafin lokacin zaben na shugaban FIFA.

Za a gudanar da wannan zabe a lokacin babban taro na musamman na FIFA da za a yi ranar 26 ga watan Fabrairtu na 2016 a birnin Zurich.

XS
SM
MD
LG