Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalolin Rayuwa Basu Hana Mutun Zama Wani Abu A Rayuwa


Almustapha Almustapha
Almustapha Almustapha

Almustapha Almustapha dan Najeriya da ya kirkiri mutun mutumi ya cigaba da baya nai kamar haka. Na halarci zama na farko daga dalibban da za’a tantache wanda wani Doctor daga kasar ta Kansas ya jagoranta Zaman ganin chewa daga shirin da ya gabata na fitar da yara waje kamar an saka son rai da sani wurin saka wadanda basu chanchanta ba. Sai aka tsara chewa sai wanda yachi jarabawar TOFL(Test of English as a Foreign Language).

A wannan tsarin ne aka daukemu kusam mu Arba’in da Shidda (46) zuwa Kaduna domin rubuta jarabawar, inda daga cikinmu mutun goma sha uku(13) kawai sukayi nasara. Bayan na shiga shekara ta biyu a jaami’ar Usmanu Danfodiyo achikin karatun physics sai aka kiramu domin zuwa neman visar karatu a kasar America (F1). A hakan aka dauki mutun goma (10) daga chikin sha ukku (13) da sukayi nasarar jarabawar zuwa U.S. Embassy Abuja domin visa.

Bayan Isowa ta a U.S. na fara karatun “Information Technology” a wata makaranta da ke karamar hukumar “Johnson County Community college” inda nayi shekara daya na fahimci cewa ban cancanta da wurin Ba. Sai Na Nemi Admission a jami’ar jihar Missouri Kansas City. Bayan na koma wannan jami’ar lokacin ne na koma karatun Degree biyu a lokaci guda na “Electrical and Computer Engineering” wanda nake tuanin shine hakikanin abunda rayuwata keson yi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG