Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Likitanci Yafi Kamata Da 'Yaya Mata


Halima Rabiu
Halima Rabiu

Halima Rabiu, 'yar asalin garin Babura, ce a jihar Jigawa, yanzu haka tana karantun aikin likitanci a jami’ar jihar Minnesota, ta nan kasar Amurka. Babban abun da ya bata sha’awar karatun likitanci shine, a lokacin da take yarinya, tana ganin yadda likitoci ke taimaka ma yara da manya. Hakan ya jawo hankalin ta da aikin likitanci.

Tana fatar ta kammala karatunta na aikin likitanci a bangaren yara, domin kuwa tana ganin akwai bukatar irin wadannan likitoci, musamman a gida Najeriya. A nata ganin, karatun aikin likitanci na mata ne, domin kuwa su suka san yadda yakamata a taimaka ma marasa lafiya da ma sauran al’uma. Don haka akwai bukatar matasa su maida hankali wajen neman ilimi don ciyar da kasa gaba.

A irin matsaloli da take fuskanta a karatun ta kuwa, babu kamar yadda suke karatu ba kaukautawa, dole ne mutun yayi karatu mai yawa, amma dai suna iya kokarin su wajen ganin sun zama daya daga cikin mafi can-canta, a wannan makarantar tasu. Ta kara da cewara a wannan zamanin kada namiji ya auri mace da bata da ilimi, haka suma ‘yan matan su tsaya sai mai ilimi, domin kuwa haka zai sa a samu al’uma mai nagarta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG