Iyalan Mr. Karl Andree, wani dan Ingila da aka kama da kwalbar giya, a cikin motar shi a Riyadh, babban birnin Saudiyya su na rokon Firaministan Ingila David Camaron, da ya roki gwamnatin kasar Saudiyya, kar ta yi ma dan’uwansu bulala dari uku da hamsin (350), bisa dalilin samun shi da kwalbar giya da aka yi. A watan Agusta na shekarar da ta gabata ne dai aka kama Mr. Karl, kuma ya na da masaniyar wannan birni ne da ba a shan giya.
Yanzu dai haka yana daure a gidan kurkuku na Jan-gari Briman, wannan gidan yarin dai ya yi kaurin suna wajen azabtar da mutane. Don haka, suna rokon kada gwamnatin Saudiya, ta zartar mishi da wannan hukuncin a bainar jama’a.
Ya na dai aki ne da wani kamfanin hako mai a kasar. Ya na da ‘yaya uku, dan shi Hugh mai shekaru arba’in da shida (46), da Kirsten mai shekaru arba’in da biyar (45), kana da Simon mai shekaru talatin da uku (33), sun ce wannan hukuncin zai iya zama sanadiyyar mutuwar baban na su, domin kuwa ya tsufa da yawa. Sun shafe watanni su na ta bi ta hannun gwamnatoci don a gafarta ma baban nasu, amma dai har yanzu haka ba ta cinnma ruwa ba.